ZABEN IRAQI DA MAKOMAR KASAR NAN GABA | Siyasa | DW | 31.01.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZABEN IRAQI DA MAKOMAR KASAR NAN GABA

Duk da barazanar da `yan tawayen Iraqi suka yi na yi wa zaben da aka gudanar a kasarsu zagon kas dai, dimbin yawan jama'a ne suka fito suka ka da kuri'unsu a ran 30 ga watan Janairu. Kusan mutane miliyan 14 ne suka ka da kuri'u a rumfunan zabe dubu 5 da dari 2 a duk fadin kasar.

Masu ka da kuri'u a rumfunan zabe a kasar Iraqi.

Masu ka da kuri'u a rumfunan zabe a kasar Iraqi.

An dai sha yin zabe a kasar Iraqi, amma, musamman ma dai a lokacin Saddam Hussein, ana iya sanin yadda sakamamakon zai kasance kafin ma ranar jefa kuri’ar. Ko kuma, idan sakamakon bai gamsad da mahukuntan kasar ba, sai a soke zaben ma gaba daya – kamar dai yadda aka yi a shekarar 1954. Ashe kuwa da ba zai ba kowa mamamki ba, da mafi rinjayin `yan kasar sun yi zamansu ne abinsu, suka ki ka da kuri’u a zaben da aka gudanar din.

A daura da zabukan baya ma, wannan zaben na da wata kasada, wato ta barazanar halaka masu ka da kuri’un da `yan tawayen kasar suka yi. Har ila yau dai, babu kuma tabbas na cewar, bayan an gudanad da zaben, za a sami wani gagarumin sauyi a Iraqin. Duk da hakan dai, dubban `yan kasar ne suka fito suka ka da kuri’unsu. A wannan huskar kuwa, sun cancanci yabo ainun, saboda ko a kasashen da ake ganin dimukradiyya ta zaunu ma, ba a samun yawan masu kada kuri’u irin na jiya a Iraqin.

Bambancin da akwai tsakanin kasashen dimukradiyya na Turai da na Amirka da wannan zaben da al’umman Iraqi suka yi jiya shi ne: A kasashen yamman, jama’a na zuwa ka da kuri’u, saboda ya zame musu kamar wani nauyi ne da ya rataya a wuyarsu. Amma `yan kasar Iraqin sun ga zaben ne kamar wata damar bayyana ra’ayoyinsu a fagen siyasa, inda za su kasance sai an dama da su, kafin al’mura su dinga tafiya daidai a kasar.

Babu dai wadanda za su fi samun fa’idar wannan zaben kamar `yan shi’iti da Kurdawa, wadanda a da, su ne aka yi musu saniyar ware a kasar. A karo na farko dai, mabiya darikar shi’iti na Iraqin, za su sami damar rike madafan iko a kasar, damar da da can, duk da rinjayin da suke da shi na yawan al’umma, ko mafarkin samunta ma ba sa yi. Kazalika ma, Kurdawan kasar na sane da wannan damar da suka samu a halin yanzu. Nan gaba dai, ba za a iya yanke wata muhimmiyar shawara a Iraqin ba tare da an dama da wadannan bangarorin biyu ba.

Ko da yake, za a iya cewa, zaben ba shi da cikakken ma’anar da ake ta yi masa kururuwar samu, saboda kaurace masa da mabiya darikar sunni suka yi, har ila yau dai babu abin da ke hujjanta kira ga kawad da darajarsa. Duka-duka dai, mabiya darikar sunnin Iraqin ba su fi kashi 20 cikin dari na al’umman kasar ba. Kuma ba dukkansu ne suka ki zuwa ka da kuri’unsu ba. Sai dai da yawa daga cikinsu sun tsorata ne, saboda barazanar da `yan tawayen suka yi na halakad da su, idan suka fita zuwa ka da kuri’u. Sabiili da haka, wajibi ne ga ko wace gwamnatin da za ta ja ragamar mulki a kasar, ta ga cewa su `yan wannan bangaren na al’umman Sunni, ba a barsu a baya ba, a yunkurin sake gina kasar da za a yi.

Babu shakka, wannan zaben kawai ba zai hana `yan tawayen Iraqin ci gaba da munanan ayyukansu ba. Har ila yau za su ci gaba da kai hare-harensu na kunan bakin wake, inda kuma za su ritsa da rayukan fararen hula da dama, wadanda ma ba ruwansu da rikce-rikicen da ake yi.

Yawan masu zaben na jiya dai, na nuna wa `yan tawayen cewa, ba su da cikakken goyon baya a bainar jama’a. Nauiyn ganin an tabbatad da tsaro da zaman lafiya kuma, zai rataya ne a wuyar sabuwar majalisa da gwamnatin da aka zaba. Ka da kuri’un da al’umman Iraqin suka yi, ba wata alama ce ta yin amanna da wanzuwar dakarun mamaye a kasar ba. Babu dai abin da zai hanzarta janyewar dakarun, kamar daukar nauyin siffanta makomar siyar kasarsu da kansu, da al’umman Iraqin gaba daya za su yi.

Zaben da aka gudanar dai, shi ne farkon mataki a wannan huskar.

 • Kwanan wata 31.01.2005
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvdP
 • Kwanan wata 31.01.2005
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvdP