Zaben gundumomi a Taiwan | Labarai | DW | 03.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben gundumomi a Taiwan

An fara kada kuri´a a zaben shugabannin kananan hukumomi da na gundumomi a birane 23 a Taiwan. Zabukan na yau asabar wanda kuma ake sa ran samun sakamakon sa a wani lokaci yau din nan wata alama ce ta goyon bayan da shugaba Chen Shui-Bian ke samu a wajen jama´ar kasar. Ko da yake a baya bayannan ya fuskanci koma baya musamman a dangane da wani binciken cin hanci da rashawa da ya shafi aikin gina hanyoyin jirgin karkashin kasa a birnin Kaosiung. Jam´iyar sa ta Democratic Progressive Party na goyon bayan samun ´yancin Taiwan. Shugaba Chen ya ce duk wata nasara da jam´iyar ´yan kishin kasa ta Kuomintang zata samu barazana ce ga ´yancin wanzuwar Taiwan. A halin da ake ciki jam´iyar Chen na da kujeru 10 yayin da Kuomintang ke da kujeru 13 na kananan hukumomi.