Zaben gama gari a kasar Pilipin | Labarai | DW | 09.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben gama gari a kasar Pilipin

Kimanin mutane miliyan 55 ne suka yi rijista dan zaben 'yan takara 45,000 wadanda ke neman kujeru 18,000 a matakai daban-daban na gwamnati.

Philippinen Wahlplakaten

Wurin ayyukan zabe a Pilipin

A wannan Litinin din al'ummmar kasar Pilipin sun fita domin kada kuri'a a zaben gama gari. Kimanin mutane miliyan 55 ne suka yi rijista, inda za su zabi 'yan takara 45,000 wadanda ke neman kujeru 18,000 tun daga matakin tarayya har zuwa kananan hukumomi. Shugaban kasar mai barin gado Benigno Aquino III na nuna goyon bayansa ga tsohon sakataren harkokin cikin gida Mar Roxas tare da adawa da dan takarar shugabancin kasar Rodrigo Duterte wanda ya bayyana a matsayin barazana ga demokradiya a kasar, bayan da ya nuna cewa zai iya rushe majalisa muddin za ta zama barazana ga ayyukan da ya sanya a gaba idan ya samu nasarar darewa a madafun iko.