Zaben fitar da gwani na shugaban kasa a jammiyar PDP a Nigeria | Labarai | DW | 16.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben fitar da gwani na shugaban kasa a jammiyar PDP a Nigeria

A yanzu haka dai an kammala dukkan shirye shirye a jammiyar PDP mai mulkin tarayyar Nigeria,domin gabatar da Gwamna Umaru Yar adua a matsayin dan takara dazai gaji shugaba Olusegun Obasanjo ,a zaben fitar da gwani dake gudana a yau.Gangamin jammiyar ta PDP wanda yazo watanni kalilan gabannin zaben kasa,ya zame wani dandalin da aka rigaya aka tsara,tunda akasarin yan takara a karkashin tutar jammiyar PDP sun janye,sakamakon matsin lamba daga Obasanjo.Wannan na nufin cewa Gwamna Umaru yar Aduwa na jihar Katsinan wanda ke zama tsohon malamin makaranta,shine dan takaran gwamnati das ake ganin zai zame shugaban Nigeria,wadda ke zama kasar datafi kowace yawan alumma a nahiyar Afrika,a zaben watan Aprilu.