1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben fidda gwani a jihohi 11 na Amirka

Gazali Abdou TasawaMarch 1, 2016

A wannan Talatar ce ake gudanar da zaben fidda gwani a jihohi 11 na Amirka wanda kuma ke zama muhimman zabe ga makomar 'yan takarar neman shugabancin kasar.

https://p.dw.com/p/1I4a2
Nevada Las Vegas Caucus
Hoto: Getty Images/AFP/J. Edelson

A Amirka a wannan Talata ce ake gudanar da zaben fidda gwani a jihohi 11 na kasar wanda kuma ke zama muhimman zabe ga makomar 'yan takarar neman shugabancin kasar a babban zaben fidda gwani na jam'iyyu wanda zai wakana a watan Yuli mai zuwa.

Alkalumma binciken jin ra'ayin jama'a dai na dora Donald Trump a sahun gaba a bangaren 'yan takarar jam'iyyar Republicain bayan da a baya ya lashe zabe a jihohi uku daga cikin hudu, yayin da a bangaren jam'iyyar Democrat Hillary Clinton ke da kwarin gwiwar samun nasara kan abokin hamayyarta Sanata Bernie Sanders a zaben na jihohi 11 da zai gudana a yau.

Ko da yake sakamakon zaben na jihohin 11 na wannan Talata ba shi ne na karshe ba amma dai ana ganin zai kasancewa zakaran gwajin dafin 'yan takarar ga kokarinsu na ganin jam'iyyun nasu sun tsayar da su a matsayin 'yan takararsu a zaben shugaban kasar ta Amirka na Nowamba mai zuwa.