Zaben Bangladash a Janairu 2007 | Labarai | DW | 27.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben Bangladash a Janairu 2007

Hukumar zabe ta kasar Bangladash ta sanar da gudanar da zaben kasa baki daya a ranar 21 ga watan janairu idan mai duka ya kaimu,duk da zanga tzangar da dubban alummomin kasar keyi na bukatar Komitionan harkokin zaben yayi murabus da mukaminsa.Masu boren sunyi dafifi ne a fadar gwamnatin kasar dake birnin Dhaka,inda suke neman gwamnati tayiwa dokokin zaben kasar garon bawul,tare da bukatar a kori komissiononin zabe guda 3,saboda zarginsu da marawa tsohon premia Khaleda Zia ,baya.Masu gangamin dai magoya bayan hadin gwiwan jammiyun adawa guda 14 ne ,dake karkashin jagorancin babban abokin hamayyan Ziya,tsohon premier Sheikh Hasina.Sakataren hukumar zaben Bangladash Abdurrashid Sarker,ya fadawa manema labaru cewa ,ba ja da baya adangane da gudanar da zaben na watan janairu.