zabe a Palasdinu | Siyasa | DW | 25.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

zabe a Palasdinu

A yau al'umar Palasdinu ke zaben majalisar dokoki

Zaben Palasdinu

Zaben Palasdinu

Binciken ra’ayin jama’a da aka yi ya ba wa kungiyar Hamas kashi 30% na jumullar kuri’un da za a kada a zaben majalisar dokokin Palasdinawan a yau laraba. To sai dai a bangaren Isra’ila ana daridari da tsayawa takarar zaben da kungiyar mai tsananin kishin addini tayi. Dangane da yawan mutanen da zasu fita domin kada kuri’unsu kuwa Mahadi Abdel Hadi, shugaban cibiyar nazarin manufofin Palasdinawa a gabacin Kudus cewa yayi lamarin ya danganta ne da yanayin da za a fuskanta, idan har an fuskanci ruwan sama ko kuma ma dussar kankara, hakan zai zama gobarar titi ga kungiyar Hamas. Saboda ita ce kadai ta tanadar da motocin bus take kuma da ikon jigilar masu zaben zuwa rumfunan zaben a duk lokacin da zarafi ya kama. Kimanin Palasdinawa miliyan daya da dubu 400 ne ke da ikon kada kuri’a a zaben na yau laraba, wanda ya kunshi jam’iyyu 14 da kuma da yawa daga ‘yan takara masu zaman kansu. Sai dai kuma kungiyoyi ko kuma jam’iyyu masu tasiri daga cikinsdu su ne Fatah ta shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas da kuma kungiyar Hamas da ta shiga takarar zaben karkashin taken:Sabon yanayi na canji da garambawul. A cikin wani bayani da yayi Mahdi Abdel Hadi ya bayyana imanin cewar kungiyar ta Hamas ba makawa za a dama da ita a sabuwar gwamnatin da za a nada nan gaba a yankunan Palasdinawan.

Gaba daya ina mai kyautata zaton cewar za a yi kafada-da-kafada ne tsakanin Fatah da Hamas. Na yi imanin cewar Fatah zata samu wakilcin mutane 62 sannan ita kuma Hamas ta samu wakilai 58, sannan ragowar kujeru 12 da suka yi shaura za a danka wa sauran jam’iyyun. Kazalika na sikankance cewar ba makawa wata gwamnati ta hadin guiwa ce za a nada tsakanin Fatah da Hamas.

Ita dai Isra’ila babban abin dake ci mata tuwo a kwarya shi ne nasarar da kungiyar Hamas zata iya samu daga zaben. An saurara daga bakin tsofon ministan harkokin wajen Isra’ilar Shimon Peres yana mai bayanin cewar:

Komene ne dai sakamakon zaben zai kasance, nasarar kungiyar Hamas zai zama babbar matsala. Mu dauka cewar Hamas ce ta lashe zaben, ko da yake ban sikankance da hakan ba. Amma shin idan an danka mata alhakin kafa gwamnati zata ci gaba da zama wata kungiya ce ta ‘yan ta’adda? Shin wa zai shiga shawarwari da ita? Wa zai yarda ya zauna da masu kai farmakin bamabamai kan teburin shawara guda. Wa zai dauki nauyin ma’aikatan hukumar Palasdinawa su kimanin dubu 150. Kazalika a ganina ba ma zata yiwu a kafa wata gwamnati ta hadin guiwa da ita ba.