1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe a kasar Mauritaniya

March 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuPx

A yau alúmar Mauritaniya ke kada kuriá a zaben shugaban kasa da nufin maido da mulkin dimokradiya a kasar ta Afrika dake yammacin Sahara. A shekarar 2005 sojoji suka yi juyin mulkin a kasar wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na shugaba Maaouiya Ould Taya. Mutane kimanin miliyan daya ne wadanda suka cancanci kada kuriá ke kada kuriár su a rumfunan zabe da aka tanada a fadin kasar. Yan takara 19 ke fafatawa a zaben shugaban kasar wadanda suka hada da masanin tattalin arziki Sidi Ould Sheikh Abdallah da kuma tsohon madugun adawa Ahmed Ould Daddah. Idan babu dan takarar da ya sami kashi 50 cikin dari na adadin kuriún da aka kada ba, to zaá sake kaiwa ga zagaye na biyu. Sojojin sun haramtawa kan su shiga takarar domin tabbatar gaskiyar aniyar su ta mayar da mulki ga farar hula. Yan kasar na fatan dukkan wanda aka zaba a matsayin sabon shugaban kasa ya tabbatar da rabon arzikin kasa daidai wa daida a tsakanin dukkan alúmomin kasar.