Zabe a kasar Haiti | Labarai | DW | 07.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zabe a kasar Haiti

A yau ake jefa kuria a zaben kasar Haiti.

Yanzu haka sojojon MDD dake kasar tun 2004,sun kammala shirye shiryen tabbatar da komai ya tafi dai dai a lokacin zaben,wanda ake sa ran masu jefa kuria kusan miliyan 3 da rabi zasu fito su kada kuriarsu a zaben kujeru 129 na majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan yayi kira ga dukkan bangarorin kasar da su amince da sakamakon zaben da zai fito.

Hakazalika kasar Amurka wadda ta baiwa kasar gudumowar dala miliyan 30 domin wannan zabe ta ce wannan zabe dama ce ga kasar Haiti ta sake tsara makomarta.

Sau 4 ake dage zaben cikin tashe tashen hakula ,amma a wannan karo jamian Majalisar Dinkin Duniya sun baiyana imanin cewa zaben zai gudana lami lafiya kodayake sunce akwai yiwurar kananan tashen tashen hankula a wasu sassa na kasar.