Zabe a kasar Georgia | Labarai | DW | 05.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zabe a kasar Georgia

Al’uman kasar Georgia sun kaɗa kuri’u a zaben shugaban kasa. Tun a watan nuwamban shekara ta 2007 Shugaba Mikhail Saakashvili ya kira zaben gaba ga wa’adi bayan wata zanga-zanga da ta gudana a babban birnin Tiblisi, inda jami’an tsaro suka yi amfani da karfin hatsi wajen tarwatse masu zanga-zangar. Ko da yake ana kyautata zaton cewar shugaba Saakashvili zai lashe zaben na yau, inda yake karawa da wasu ‚yan takara guda bakwai, amma wani bincike da aka gudanar a ‚yan kwanakinnan ya nuna cewar mai yiwuwa ya kasa samun kashi 50 cikin dari na kuri’un da zai bashi damar ɗare kujerar Prain Minista ba tare da an sake wani zabe nan da makwanni biyu ba.