Zabe a kasar Finnland | Siyasa | DW | 14.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zabe a kasar Finnland

A zaben da al'umman kasar za su ka da kuri'u a ran 15 ga wannan watan, don zaben shugaban kasa, hasashe nanuna cewa shugaba mai ci yanzu, Tarja Halonen za ta iya samun nasara. Sai dai, babu tabbas ne ko za ta iya samun cikakken rinjayi ba da an sake yin zabe a zagaye na biyu ba ?

Shugaba Tarja Halonen ta kasar Finnland.

Shugaba Tarja Halonen ta kasar Finnland.

Tarja Halonen, shugabar kasar Finnland mai ci a yanzu, na kyautata zaton cewa, za ta iya lashe zaben kasar a karo na biyu. A yau ne dai al’umman kasar za su ka da kuri’u don zaban shugaban kasa. Sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar kafin ranar zaben dai na nuna cewa, shugaba Halonen ce ke kan gaba da kashi 51 cikin dari. Gibin da ke tsakaninta da abokin hamayyarta kuma ya kai kashi 30 cikin dari. Sabili da haka ne dai, magoya bayan shugaban mai shekaru 62 da haihuwa, suka hakikance cewa, ita ce za ta sake lashe zaben. Sai dai, babu tabbas ne ko za ta iya samun cikakken rinjayi, a zagaye na farko, ko kuwa sai an sake gudanad da wani zaben kuma a zagaye na biyu. Tarja Halonen dai, ta shiga takarar zaben ne karkashin tutar jam’iyyar `yan gurguzu ko kuma Social Democrats, wadda kuma ke samun goyon bayan jam’iyyun neman sauyi da kungiyoyin kwadago. Manufofinta dai sun fi ba da karfi ne wajen inganta halin rayuwar jama’ar kasar. Kamar dai yadda ta bayyanar:-

„Manufofinmu na inganta halin rayuwar jama’a a nan Finnland dai, suna nuna adalci ga duk al’umman wannan kasar. Su ne kuma, ke bai wa Finnland fa’idar da take samu a tsereriniyar kasuwanci. Nan gaba ma, zan ci gaba da dagewa ne, wajen kare hakkin da `yan kasar Finnland ke da shi na samun aikin yi, da kyakyawan halin tsaro da kuma jin dadin rayuwa.“

Sauran jam’iyyun kasar dai na duk iyakacin kokarinsu wajen kalubalantar shugaba Halonen a zaben. Jam’iyyar tsakiya, ta tura Firamiyan kasar Matti Vanhanen ne shiga takarar zaben, yayin da jam’iyyar `yan mazan jiya kuma, suka tura shugaban bankin zuba jari na Turai, Sauli Niinistö tamkar dan takaranta. A halin yanzu dai, bisa alkaluman baya-bayan nan da aka buga, shi Niinistön na gaban Firamiya Vanhanen, abin da kuma ke nuna cewa, idan ya kai ga gudanad da zabe a zagaye na 2, dan takaran jam’iyyar `yan mazan jiyan, wato Niinistön ne zai tsaya tamkar abokin hamayyar shugaba Halonen. Amma ko yaya sakamakon zaben na yau ya kasance, da alamun cewa, ita Halonen ce za ta fi samun yawan kuri’u. Har ila yau, tana da magoya baya da yawa, wadanda suka ka da mata kuri’u a zaben da aka gudanar shekaru 6 da suka wuce, inji wani tsohon shaihin malamin fannin siyasa a jami’ar Finnland din, Farfesa Tuomo Martikainen:-

„Akwai mutane da yawa, wadanda har ila yau suka gamsu da irin salonta na tafiyad da harkokin mulki. Ita Halonen din da kanta kuma, tana kwatanta kanta ne da cewa, ita shugaban duk al’umman kasar ne, ba na wadanda suka zabe ta ba kawai. Cudanyar da take yi da jama’a a ko yaushe, ya sa ta sami farin jini sosai.

Kundin tsarin mulkin kasar Finnland din dai, ya tanadi cewa, shugaban kasar ne kuma zai dinga kula da manufofin harkokin waje, tare da tuntubar gwamnati. Shugaban na kuma da `yancin yi wa fursunoni afuwa. Bugu da kari kuma, shi ne ko kuma ita ce kwamdan rundunonin sojin kasar. Sabili da haka ne batun tsaro, ya zamo daya daga cikin muhimman jigogin yakin neman zabe. A daura da wasu bangarorin da ke ganin Rasha tamkar wata barazana ga Finnland din a huskar soji, abin da ya sa kuma suke kira ga shigarta cikin kungiyar NATO, shugaba Tarja Halonen na watsi da duk wadannan ra’ayoyiin biyu. A nata ganin dai:-

„Nauyin da ya rataya a wuyar Finnland ne ganin cewa, an samar wa duniya wani yanayi na tabbatad da adalci a ko’ina. Saboda idan aka sami adalci a duniya, babu shakka za a sami kuma zaman lafiya.“

Masu sukar lamiri dai na zarginta ne da kasancewa mai bin akidar shucin gizo, wadda ta fi mai da hankalinta kan batutuwan kasa da kasa da ba su da wani tushe, maimakon kulawa da kare maslahar kasar ta Finnland.

To ana jira ne dai a ga sakamakon da zaben na yau zai haifar. Ita jam’iyyar Social Democrats, wadda ta tura shugaba Halonen kamar `yar takararta, tana kyautata zaton cewa, za ta sami cikakken rinjayi a karo na farko, ba tare da sai an koma zagaye na biyu ba kafin a zabi shugaban kasa. Ko za ta iya cim ma wannan burin kuwa ?