1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe a kasar Amurka

Hauwa Abubakar AjejeNovember 7, 2006

A yau yan kasar Amurka suke zaben yan majalisun dokoki ,yayinda yan jamiyar democrats suke kokarin ganin sun kwace majalisun daga hannun yan jamiyar republicans

https://p.dw.com/p/BtxV
Hoto: AP

Su dai shugabannin jamiyar democrats sunyi hasashen cewa zasu sake kwato majalisar wakilai karo na farko tun 1994,amma kuma suna bukatar kwashe mafi yawa kafin su samu kwato majalisar dattijai

Dukkanin bangarorin dai sun samu fitowar magoya bayansu da adama a kuriar ta yau.

Shugaban komitin kasa nay an democrats howard Dean ya baiyana imaninsa cewa zasu lashe zaben majalisar wakilai,sai dai yaki cewa komai game da majalisar dattijai.

A zaben na yau dai matsalolin injunan zabe da suka faru a zabukan 2000 da kuma 2004,sun sake kunno kai a yau,jim kadan bayan bude runfunan zabe.

A wata makarantar lardin Cleveland jihar Ohio inda bakar fata suka fi yawa dukkanin injunan zabe 12 sun daina aiki,gab da fara jefa kuriun,sai bayan saoi 2 da fara zabe suka fara aiki.

Hakazalika an samu irin wadannan matsaloli a wasu jihohi da suka hada da New York,Pennsylvania da Florida.dukkaninsu jamiyaun 2 dai sun aike da lauyoyi da zasu kalubalanci duk wani magudi nan take.

Batutuwan wariyar launin fata da kuma musamman yaki da taaddanci da kuma halin da ake ciki a Iraqi inda fiye da sojin Amurka 2,800 suka halaka,su suka mamaye yekuwar neman zabe na jamiyun.senator Chuck Schumer na jamiyar democrats yace wannan itace dama ta karshe da zasu koyawa Bush darasi,saboda duk da shekaru 6 na mummnunan shuagbanci,har yanzu babu wanda ya kama da wani laifi daya da ya aikata.

Shi kuma Bush a nashi kanfe ya zargi abokan hamaiyarsa cewa,basu da aniyar samun nasara a wannan yaki saboda haka a cewarsa ya kamata Amurkawa su zabi jamiyarsa muddin dai suna neman cikakken kariya daga yan taadda.

Baya ga batun Iraqi sakamakon zaben ya kuma dogara ne akan batun kula da lafiya,tattalin arziki da batun bakin haure.

Yawancin kuriar jin raayi da kuma kwarraru sunyi hasashen cewa jamiyar democrats da alamu zata samu rinjaye a zaben.

Kuria na baya bayan nan don jin rayin jamaa da aka gudanar ya baiwa jamiyar democrats kashi 51 jamiyar republicans kuma kashi 45.