Zabe a France | Labarai | DW | 20.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zabe a France

‘Yan takarar kujerar shugaban kasa a Faransa sun kamalla shirye shirye akan zaben da za’a gudanar ranar lahadi mai zuwa. A jiya alhamis ne dan takara Nicolas Sarkozy yayi rangadin sa na karshe tare da goyan bayan manyan ‘yan kwallon kafa da kuma tsohon prain-minista a birnin Marseil. A yayin da abokiyar adawar sa Segolene Royal ta kamalla nata kampen a birnin Toulous, inda matar tsohon shugaban kasar Faransa Daniel Miterand da prain-ministan kasar Spain Jose Luis Zapatero suka yi mata rakiya. Sakamakon binciken ra’ayin jama’a da aka gudanar ranar 6 ga watan maris da ya gabata, ya nuna cewar Sarkozy ne zai lashe zaben, inda Sagolene Royal zata yi ta biyu.