1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe a faransa

May 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuLv

Rahotanni daga kasar faransa na nuni dacewa mafi yawa daga cikin alummomin kasar da suka cancanci kada kuria milion 44 ne ,suka kada kuriunsu a zaben zagaye na biyu na shugaban kasa tsakanin Nicholas Sarkozy da Segolene Royal.Kawo yammacin yau dai akalla kashi 75 daga cikin 100 na yawan masu zaben ne suka rigaya suka kada kuriunsu,adangane da zaben wanda zai gaji shugaba Jacques Chirac na faransa.Manazarta dai sun bayyana tururuwan jamaa zuwa cibiyoyin zaben da kasancewa na farkon irinsa a shekaru 30 da suka gabata, na tarihin zabe a faransan.Virginie Reche dai na daya daga cikin magoya bayan Sarkozy…..

„Ina ganin kowa yana cikin zumudi adangane da wannan zabe.Abun mamaki ne a wannan karon ,da kowa ya shiga gadan gadan.a bangare na ina fatan dan takara Sarkozy ya lashe wannan zaben“