za´a shigar da Kasar Montenegro cikin yayan kungiyyar Eu | Labarai | DW | 17.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

za´a shigar da Kasar Montenegro cikin yayan kungiyyar Eu

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar cewar ta yanke shawarar shigar da kasar Montenegro a matsayar member ta 47. Wannan yazo dai dai shekara daya bayan kasar at samu ‚yancin kai daga tarayyar Serbia. An tsayar da ranar 11 ga watan mayu akan shigar da ita a kungiyar inji wata majiya daga zauren taron ‚yan majalisar dokokin a birnin Strassbourg. Ko dayake majiyar ta kara da cewar kasar ta Montenegro ta samu cigaba matuka a fannin demokradiya, amma dole ne ta hamzarta wajen gabatar da sabon kundin tsarin kasar.