Zaa sako wadanda ake garkuwa da su a Naija Delta | Labarai | DW | 08.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaa sako wadanda ake garkuwa da su a Naija Delta

Yan kungiyoyin sa kai a yankin Naija delta a Nijeriya sunyi alkawarin sako yan kasar Koriya ta kudu su 5 da suka yi garkuwa da su a jiya laraba.

Wannan kuwa ya biyo bayan kira da shigabansu Asari Dokubu wanda yanzu yake tsare yayi masu na sakin wadannan mutanen.

Dukkanninsu yan kasar ta koriya ta arewa da yan ta kifen suka sace,suna aiki ne da kanfanin Deawoo,kuma sun sace sune suna masu kira da a sako Alhaji Asari,wanda yake fuskantar zargin cin amanar kasa.