Za´a rataye ″Chemical Ali″ a cikin kwanaki 30 masu zuwa | Labarai | DW | 04.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za´a rataye "Chemical Ali" a cikin kwanaki 30 masu zuwa

Kotun kolin kasar Iraqi ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yankewa Ali Hassan al-Majid wanda aka fi sani da Chemical Ali da wasu jami´ai biyu na tsohuwar gwamnatin Saddam Hussein. Tun a ranar 24 ga watan yuni aka yankewa mutanen 3 hukuncin kisa bayan an same su da laifin kisan kare dangi da cin zarafin bil Adama. Su na da hannu a kisan kare dangi da aka yiwa Kurdawa a yankin Anfal a shekara ta 1988. Ana iya aiwatar da wannan hukunci akan su ta hanya ratayawa a ciki kwankai 30 masu zuwa kamar yadda dokar Iraqi ta tanada.