Za´a nada Tony Blair a mukamin wakilin zaman lafiya a GTT | Labarai | DW | 26.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za´a nada Tony Blair a mukamin wakilin zaman lafiya a GTT

Za´a bawa FM Birtaniya mai barin gado Tony Blair mukamin sabon wakili na musamman na bangarorin nan hudu dake shawarta batun zaman lafiyar yankin GTT. Majiyoyin jimi´an diplomasiya a Turai sun ce bisa ga dukkan alamu za´a nada Blair akan wannan mukami a gun wani taro da wakilan bangarorin zasu yi yau a Birnin Kudus. Rahotanni daga Washington sun ce tuni har wakilan kasashen Amirka, Rasha da na KTT da MDD sun kammala dukkan shirye shiryen bawa Blair wannan mukami. Aikin sa dai zai kasance ne ba da gudunmmawa musamman game da kafa wata ´yantacciyar kasar Falasdinu.