Za´a matsawa Syria lamba har sai ta ba da hadin kai a binciken kisan Hariri | Labarai | DW | 25.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za´a matsawa Syria lamba har sai ta ba da hadin kai a binciken kisan Hariri

Amirka da Birtaniya da kuma Faransa sun ce zasu matsawa gwamnatin Syria lamba don ta ba da cikakken kadin kai a binciken kisan tsohon FM Lebanon Rafik Hariri. An jiyo jakadan Amirka a MDD John Bolton na cewa kasashen 3 sun goyi da bayan zartas da wani kudurin MDD wanda zai tilastawa Syria ta ba da hadin kai. To sai dai ba´a sani ba ko wannan kudurin zai tanadi kakkabawa Syria takunkumi. Wani taron da kwamitin sulhu na MDD zai yi a yau zai ba da karin haske game da haka. Wani rahoton binciken MDD da aka bayyana a makon jiya ya zargi manyan jami´an gwamnatin Syria da hannu a fashewar bam din da ya halaka Rafik Hariri da wasu mutane 20 a cikin watan fabrairu da ya gabata. To sai dai kasar ta yi watsi da wannan zargi tana mai cewa yana da manufa ta siyasa.