1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaa gudanar da wani taro kan sasanta rikicin darfur a abuja nigeria

mansour Bala BelloAugust 20, 2004

A yanzu haka kUngiyar taraiyar Afrika ta dauki gabarar gudanar da wani taro a abuja a Nigeria domin warware rikicin lardin DArfur a Sudan a ranar Litinin mai zuwa .

https://p.dw.com/p/Bvh9
Hoto: Patrick Vanhule

Tun ba yau ba dai kwamitin tsaro na mdd ya bawa kasar ta sudan waaadin wata daya ta dakatar da wannan yamutsi idan ba haka ba kuwa ta yabawa Aya zakinta na kakaba mata takunkumin tattalin arzikin kasa ..To sai dai domin cimma wannan manufar na kwance damarar yaki a tsakanin bangarorin biyu a yanzu haka kungiyar taraiyar Afrika na cigaba da tuntubar juna domin warware rikicin baki daya .Bugu da kari a yanzu dai kungiyar ta Au a takaice na bukatar ganin cewa gwamnatin sudan ta amince da dakarun kungiyar sama da dubu biyu a lardin na darfur domin samun kwancuiyar hankali mai dorewa ..a dangane da haka ne shugaba obasanjo na Nigeria ya mika goron gayyata ga bangarorin domin tasttaunawa a makon gobe a Abuja domin cimma wannan manufar da aka sanya a gaba ..cikin wannan tawaghar dai ta hada da shugaban hukumar kungiyar ta au alfa oMar konare wanda zasu bar birnin Adis Ababa a ranar lahadi domin isa Nigeria kann wannan tAron to sai dai duk bangarorin biyu sun amince da halartar taron na Nigeria sai dai kuma har kawo yanzu basu daina sukan juna ba nay haddasqa wannan rikicin daya ki yaki cinyewa a kasar ta sudan ..Gwamnatin Sudan dai ta sha nanata cewa tanayin bakin kokarinta na kwance damarar yaki ga yan kungiyar janjawedd wadanda ke cigaba da haifar da rudani a kasar ta sudan musamman ta cin zarafin baskaken fatu a lardin na darfur ..Bugu da kari har yanzu dai babu tabbatas na cewa shugaban Kasar el Bashir zai amince da jibge wadannan dakarun na Afrika a lardin na darfur .A jiya dai ministan cikin gida na kasar ta sudan yace an ware a kalla wurare sama da 11 a kasar domin yan gudun hijira tare da kare lafiyarsu .Ya kuma kara da cewa a yanzu haka arewacin lardin na darfur ya kasance a cikikkin kwanciyar hankali batare wani yamutsi ba ..To sai dai da wuya wannan matakin ya birge Amurka da mDD da sauran kassashen dake jajantawa yan lardibn na darfur bisa cewa gwamnatin kasar ce ke marawa yan kungiyar janjawed baya domin aikata wannan taasa .Tun ba yanzu ba yayan kungiyar ta janjawed ke nuna halayyar rashin imani ga wadanda duk ke marawa yan tawayen lardin baya ,kungiyar dake neman yanci daga gwamnatin kasar ..A wani kiyasi da mdd tayi ta tabbatar da kisan mutane sama da dubu 30 zuwa 50 a lardin na darfur tare da haifar da kaura ga sama da miliyan daya .wAta majiya dai na cewa cututtuka sun barke a wani sansanin yan gudun hijira a Chad bayan da yan lardin suka kwarara zuwa kasar a sabili da wannan yaki .Tuni dai Kasar Nigeria ta gargadi kasar ta Sudan cewa tayi hattara bisa sakamakon kin amincewarta na warware rikicin a halin yanzu .