Za´a fuskancin babbar matsalar karancin jama´a a Jamus | Labarai | DW | 07.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za´a fuskancin babbar matsalar karancin jama´a a Jamus

Za´a fuskanci matsanancin karancin yawan al´uma a nan Jamus kafin shekara ta 2050. Sakamakon wani lissafi da ofishin kididdiga na Jamus ya bayar yau a birnin Berlin ya nunar da cewa yawan jama´a a Jamus zai ragu daga miliyan 82 a yanzu zuwa miliyan 69 ko 74 nan da shekaru 43 masu zuwa. Babban dalilin wannan ci-baya shi ne karancin haihuwa a cikin kasar. Lissafin na ofishin ya ba da la´akari da yawan ´yan ci-rani a cikin kasar wanda alkalumman suka ce zasu kai dubu 100 zuwa dubu 200 a kowace shekara. Mataimakin shugaban ofishin kididdiga na Jamus Walter Radermacher ya bayyana cewa.