1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za´a ci-gaba da gangami har sai an ga bayan gwamnatin Libanon

Shugaban kungiyar Hisbollah Sheikh Hassan Nasrallah ya fadawa dubban magoya bayan sa cewar sannu a hankali zasu kifar da gwamnatin Libanon mai samun daurin gindin kasashen yamma. Wannan sanarwa ta shugaban na Hisbollah ta zo bayan kwanaki 7 na zanga-zangar da kungiyar ta Hisbollah da masu goyon bayan Syria suka shirya da zummar kayad da gwamnatin FM Fuad Siniora. A cikin wani jawabi Nasrallah ya zargi FM Siniora da hada baki da Isra´ila a lokacin yakin nan na wata daya da Hisbollah ta yi da da kasar Yahudun Isra´ila. Ya ce FM ne ya umarci sojojin Libanon da su kwace makaman Hisbollah.