Za a tallafa wa Afganistan da kudi biliyan 15,6
October 5, 2016Kasashen duniya a kakashin jagorancin Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Amirka sun yi alkawarin tallafa wa kasar Afganistan da kudi miliya dubu 13 da miliyan 600 na Euro a cikin shekaru hudu masu zuwa domin agazawa shirin sake gina kasar da farfado da tattalin arzikinta .
Taron kasashen duniya aminnan kasar Afganistan da ya gudana a birnin Brussels ne ya sanar da daukar wannan mataki na tallafawa kasar ta Afganistan. Frederica Mogherini ita ce jagorar majalissar ministocin harakokin waje na Tarayyar Turai:
"Ta ce mu dukanmu da ke saman wannan tebiri da kamfanonin da kungiyoyi kimanin 100 a shirye muke mu agaza a cikin ko wani taki daya na tafiyar Afganistan. Mun san abin da kamar wuya, kuma tafiya ce mai nisa, amma ba za mu yi kasa a gwiwa ba"
Kasashen duniyar sun sha alwashin talfa wa kasar ta Afganistan wannan kuwa duk da hare-haren da kasar take fuskanta daga mayakan Kungiyar Taliban wadanda ke ci gaba da yin turjiya shekaru 15 bayan kawar da su daga mulkin kasar.