1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a soma shari'ar kisan Sankara

Ramatu Garba Baba
October 13, 2017

Yayin da ake sauran 'yan kwanaki kalilan kafin cika shekaru 30 da kisan tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara, kotu ta bijiro da batun shari'a kan wadanda ake zargi da hannu a kisansa.

https://p.dw.com/p/2llAa
Burkina Faso Päsident Thomas Sankara
Hoto: picture-alliance/dpa/AFP

Thomas Sankara ya rasu ne a shekarar 1987 a wani juyin mulki da hambararren shugaba Blaise Campaore ya jagoranta. Sai dai ba a taba dago batun shari'arsa ba a tsawon shekarun da Blaise Compaore ya shafe yana mulki duk da cewa tun bayan mutuwarsa an yi ta samun zanga zanga daga magoya bayansa da ma iyalansa da suka nemi a gudanar da bincike don gano da kuma hukunta duk wadanda keda hannun a mutuwar jagoran sauyi a kasar.

A shekarar 2015 aka tono gawar da ake kyauta zato na tsohon shugaban ne da zummar gudanar da bincike na tabbatar da cewa gawar ta sa ce da kuma musababbin mutuwarsa.Thomas Sankara ya kasance mutumin da ya jagoranci fafutukar 'yantar da kasar ta Burkina Faso ta hanyar bijiro da sabbin tsare tsare sai dai kafin ya cimma burinsa , Blaise Campaore ya hambarrar da shi a shekarar 1987.