Za a rantsad da shugaban kasar Zanzibar.
November 2, 2005Talla
An fara shirye-shiryen rantsad da shugaban tsibirin Zanzibar, Amani Abeid Karume, wanda ya sake cin nasara a zaßen da aka gudanar a karshen makon da ya gabata. Amma `yan jam’iyyun adawan tsibirin sun ce za asu ci gaba da zanga-zangarsu ta nuna adawa da sakamaokon wannan zabe, wanda suka ce an tabka magudi a lokacin ka da kuri’un.