Za a mika rahoto kan kisan gillan da aka yi wa Hariri ga Kofi Annan. | Labarai | DW | 20.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a mika rahoto kan kisan gillan da aka yi wa Hariri ga Kofi Annan.

A wata sabuwa kuma, a yau ne kwamitin da Majalisar Dinkin Duniya ta nada don gudanad da bincike kan kisan gillar da aka yi wa tsohon Firamiyan kasar Lebanon, Rafik Hariri, zai gabatad da rahotonsa ga babban sakataren Majalisar. Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin wani alkalin Jamus, Detlev Mehlis, ya nemi gano sanadiyya da kuma wadanda suka shirya kisan gillar da aka yi wa Rafik Hariri ne a wani harin bam da aka kai wa ayarin motocinsa a birnin Beirut a cikin watan Fabrairun da ya gabata. Kusan mutane 20 ne kuma tashin bam din ya ritsa da su har lahira.

Kasar Siriya, wadda ta janye dakarunta daga kasar Lebanon din, ta yi watsi da duk wani zargin da ake yi mata na cewa tana da hannu a wannan harin. Amma shugaban kwamitin binciken, Mehlis, ya ambaci sunayen wasu jana-janar na rundunar sojin Lebanon guda 4, masu goyon bayan manufofin Siriya a kasar, wadanda ake tuhuma da masaniya ga kisan gillar. Kazalika kuma kwamitin ya yi wa jami’an Siriya guda 7 tambayoyi. Gobe juma’a ne dai ake sa ran kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar, zai sami nasa rahoto kan binciken.

A halin da ake ciki yanzu dai, Amirka ta ce tana nazarin yadda Majalisar Dinkin Duniya za ta iya daukan wani mataki kan Siriya, saboda katsalandan da ta yi a kasar Lebanon da kuma daurin gindin da take bai wa `yan tawayen Iraqi.