Za a mayar da Salah Abdeslam Paris daga Brussels | Labarai | DW | 31.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a mayar da Salah Abdeslam Paris daga Brussels

Salah Abdeslam daya cikin maharan Paris a cewar ofishin mai gabatar da kara na tarayya a kasar ta Beljiyam ya amince da a mayar da shi Faransa.

Salah Abdeslam Fahndungsfoto

Salah Abdeslam da aka kama a Brussels bayan watanni yana buya

Mahukunta a kasar Beljiyam a wannan Alhamis sun bayyana amincewarsu da mayar da Salah Abdeslam zuwa birnin Paris na Faransa, sai dai masu gabatar da karar ba su bayyana ranar da za a kai shi birnin na Paris ba.

Salah Abdeslam a cewar ofishin mai gabatar da kara na tarayya a kasar ta Beljiyam ya amince da a mayar da shi Faransa. Yanzu kasashen biyu na duba yadda za a aiwatar da matakin kamar yadda jawabin ofishin ya nunar.

Abdeslam dan shekaru 26 da ke takardar zama a Brussels da Paris ya kasance wanda ya yi saura cikin wadanda suka kai hari a ranar 13 ga watan Nuwamba na shekarar bara wanda ya yi sanadi na rasa rayukan mutane 130 a Paris, wanda kuma a ranar 18 ga watan nan na Maris aka samu dama ta kama shi bayan watanni hudu da ya yi yana gudun buya.