1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a kulla yarjejeniyar sabuwar dangantaka tsakanin EU da AU

Ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai EU da takwarorinsu na kungiyar tarayyar Afrika AU sun ƙuduri aniyar buɗe sabon babi na dangantaku tsakaninsu. A yau rana ta ƙarshe ta taron ƙolin su a birnin Lisbon na ƙasar Portugal ɓangarorin biyu za su sanya hannu kan wata yarjejeniya bisa wannan manufa. Yarjejeniyar ta tanadi yin adalci da yin wata dangantaka ta cuɗe-ni in cuɗe ka a hulɗoɗinsu tare da ba da cikakken haɗin kai tsakanin nahiyoyin biyu. Hakazalika ƙungiyar EU zata ƙara yawan taimakon kuɗi da take bawa dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙungiyar AU. Su ma a nasu ɓangaren ƙasashen Afirka zasu ɗauki sahihan matakan kare haƙin bil Adama. Tun a jiya asabar taron na shugabannin kasashen Turai da Afirka ya tattauna game da batun kare haƙin bil Adama. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi amfani da wannan dama inda ta soki shugaban Zimbabwe Robert Mugabe da yin fatali da haƙin ´yan Adam a cikin ƙasar sa.