Za a kada kur′ar tsige Jacob Zuma | Labarai | DW | 10.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a kada kur'ar tsige Jacob Zuma

Da alama kura na neman kai bango ga shugaban kasar Afirka ta Jacob Zuma, wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar wakilan kasar za ta kada kuri'ar tsige shugaban da ga madafun iko.

Jacob Zuma dai na fuskantar wannan matsin lamban ne bayan da aka kuma bankado sabbin zarge-zargen cin hanci da rashawa na hada kai da wasu hamshakan 'yan kasuwa. To sai dai bisa ga dukkan alamu jam'iyyar ANC mai mulki na ganin tana shirye da ta fskanci dukkanin ,abinda ta kira bita kullin hsiyasa da ga jam'iyun adawan kasar, a baya dai shugaba Zuma ya cimma tsallake rigingimu masu dabaibayi.Jam'iyyar adawa ta Demokratic Alliance ce dai ta gabatar da bukatar kada kuri'ar tsige Jacob Zuma, kan abin da ta kira cin zarafin jaririyar demokaradiyyar kasar ta Afirka ta Kudu.