1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a gina sansani mafi girma a Bangladesh

Ramatu Garba Baba
October 18, 2017

Kasar Bangladesh ta sanar da bukatar gina wani sansani da zai iya tsugunar da 'yan gudun hijra akalla dubu dari takwas don magance cunkoson mutanen da suka gujewa rikici don samun mafaka.

https://p.dw.com/p/2m6H6
Bangladesch Rohingya Flüchtlinge
Hoto: Getty Images/AFP/M. Uz Zaman

Gwamnatin ta dauki matakin ne don samun damar magance kwararar 'yan gudun hijrar Rohingya na kasar Myanmar da ke tserewa rikice-rikicen kabilanci a kasarsu, ana ganin in har an yi nasarar gina sansanin zai kasance sansani na 'yan gudun hijra mafi girma a duniya. Yanzu haka 'yan gudun hijrar Rohingya fiye da dubu dari biyar ne suke samun mafaka a Bangladesh yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsaloli na daukar dawainiyarsu.

Hukumar 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana da 'yan gudun hijra fiye da miliyan sittin da biyar da ake tsugune da su a sansanonin na 'yan gudun hijra daban daban a duniya.