Za a gabatad da wasu mutane 6 gaban kotu a Birtaniya, saboda zarginsu da ake yi da gudanad da ayyukan ta’addanci. | Labarai | DW | 14.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a gabatad da wasu mutane 6 gaban kotu a Birtaniya, saboda zarginsu da ake yi da gudanad da ayyukan ta’addanci.

Jami’an tsaro a Birtaniya sun ce za a gurfanad da wasu mutane 6 daga cikin mutane 14 da aka tsare tun farkon wannnan watan gaban kotu, saboda zargin da ake yi musu na gudanad da ayyukan ta’addanci. Wata sanarwar da Hukumar ’yan sandan birnin London ta bayar ta ce, yau za a ɗaukaka ƙarar mutanen gaban kotun lardin Westminster da ke birnin. Kawo yanzu dai mutane goma ke nan ake zarginsu da ta’addancin, tun wani ɗaukin da ’yan sandan Birtaniyan suka yi a ran 1 ga wannan watan, inda suka kame mutane da dama a duk faɗin ƙasar. Har ila yau dai akwai sauran wasu mutane biyu kuma, tsare a hannun ’yan sanda, amma waɗanda ba a ɗaukaka ƙara game da su ba tukuna. Bisa dokokin yaƙi da ta’addanci na Birtaniyan dai, za a iya tsare mutanen da ake tuhumarsu har zuwa kwanaki 28, ba tare da an kai ƙararsu gaban kotu ba.