ZA A FARA TUHUMAR SADDAM HUSSAIN A WATA KOTUN IRAQI. | Siyasa | DW | 30.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZA A FARA TUHUMAR SADDAM HUSSAIN A WATA KOTUN IRAQI.

HOTON SADDAM HUSSAIN BAYAN CAFKE DA DAKARUN SOJIN AMURKA SUKAYI A WANI GIDA A GARIN TIKRIT.

default

A yanzu haka dai ta faru ta kare wai anyiwa mai dami daya sata. A tun daren jiya ne Dakarun sojin Amurka suka mika Tsohon Shugaban kasar Iraqi Saddam hussain da kuma wasu na hannun daman sa goma sha daya hannun gwamnatin rikon kwarya bisa jagorancin Faraminista Iyad Alawi.

Daukar wan nan mataki daga bangaren dakarun mamayen ya biyo bayan mika musu cikakken mulki ne da akayi kwanaki biyu da suka gabata.

A cewar Rahotanni da suka iso mana Dakarun sojin Amurka dake iraqi sune za suci gaba da lura da tsaron Saddam Hussain da mukarraban nasa su kuma shugabannin rikon kwarya na kasar su dinga bada umarni dangane da abin da ya dace ayi game da tuhumar tsohon shugaba n da mukarraban nasa.

A dai tun jiya talata ne Faraminista Iyad Alawi ya bayyana cewa a gobe Alhamis ne idan alllah ya kaimu za a fara tuhumar tsohon shugaban na iraqi dana hannun daman nasa bisa zarge zargen da ake masa na take hakkokin dan adan a lokacin mulkin sa.

A wata ganawa da shugaban da zai jagoranci kotun da zata tuhumi Saddam Hussain yayi da tsohon shugaban na iraqi a karon farko a cewar sa Saddam Hussain yace dashi barka da safiya.

Salem Cahalabi ya kuma kara da cewa saddam Hussain ya bukaci daya yi tambaya to amma Chalabi ya amsa masa da cewa ya dakata har zuwa Gobe Alhamis. Wato a Takaice dai idan anzo fara tuhumar sa ya tambayi duk abin da yake son ya tambaya.

Saddam Hussain wanda a yanzu yake da shekaru 67 ana zargin sa ne da sanadiyyar mutane yan kasar ta iraqi sama da miliyan daya a lokacin mulkin sa a hannu daya kuma da gudanar da mulkin kama karya da kuma danniya wanda hakan ya haifar aka gallazawa wasu miliyoyin yan kasar.

A cewar Salem chalabi dukkanin mukarraban na Saddam Hussain sun zamo abin tausayi yayin da aka tabbatar musu da cewa a gobe ne za a fara tuhumar su dangane da laifuffukan da suka aikata a lokacin zamanin Saddam Hussain.

Ragowar laifuffukan da za a cahji Saddam Hussain sun hadar da farwa kasar Kuwait da yaki da yayi a shekara ta 1990 a hannu daya kuma da yakin daya gudana a tsakanin kasar Iran da iraqi a shekara ta 1980 zuwa 1988.

Wanda yafi tsorata da ruduwa a cewar Salem chalabi shine Ali Hassan Al Majid wanda akafi sani da suna Kemikal Ali. Rahotanni dai sun nunar da Cewa a shekara ta 1988 kemikal Ali yayi sanadiyyar mutuwar Kurdawa a Halabja kusan dubu biyar ta hanyar amfani da hodar Ibilis.

A yanzu haka a cewar Salem Chalabi an kammala shirya masu gabatar da shaidu game da wadan nan zarge zarge da akewa tsohon shugaban na iraqi a lokacin tuhumar tasa.

A can baya dai faraminista Iyad Alawi ya tabbatar da cewa wan nan sharia ba zata dauki lokaci ba kamar yadda ake zato a can baya.

Kuma a lokacin sauraron karar gwamnatin sa a cewar Iyad Alawi zatayi iya bakin kokarin ta wajen ganin an tabbatar da adalci da gaskiya a lokacin yankewa Saddam Hussain da mukarraban sa hukunci.

Ibrahim Sani.