1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a fara biyan kudi a shafukan Facebook da Instagram

Binta Aliyu Zurmi
February 19, 2023

Kamfanin Meta mai kafofin sadarwa Facebook da Instagram zai fara karban kudi don tantance shafukan mutane

https://p.dw.com/p/4NiRL
Meta Facebook Logo
Hoto: Rafapress/Zoonar/IMAGO

Kamfanin Meta da ke da kafofin sada zumunta na zamani na Facebook da Instagram ya sanar a wannan Lahadin cewar zai kaddamar da wani tsari ga mai bukatar tantance shafinsa ko dai na Facebook ko kuma na Instargram. Sai dai tsarin zai bukaci biyan wasu 'yan kudade.

Shugaban Kamfanin Mark Zuckerberg ya ce sun fito da wannan tsarin ne domin kaucewa masu amfani da hotunan ko sunayen wasu mutanen na daban suna cewa su ne, wanda a lokuta da dama har ta kan kai ga an yi damfara da sunan wani da bai ji ba bai gani ba.

A ko wane wata alamar ta tantancewar ta Meta za ta kai dalar Amirka 12 ko kuma 15 kwatankwacin naira dubu 5 ko kusan dubu 7 ga kowane shafi.

Mark Zuckerberg ya ce wannan sabon shirin zai fara aiki ne a wannan makon da muke shiga a kasashen Australiya da NewZealand kafin daga baya su isa wasu kasashen.

Kafofin sadarwa irinsu Twitter da Snapchat da Telegram tuni suka fara wannan tsari.