Za a daure tsohon shugaban kasar Peru | Labarai | DW | 10.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a daure tsohon shugaban kasar Peru

Wani babban alkali a kasar Peru ya bada umarnin kame tsohon shugaban kasar Alejandro Toledo tare da garkameshi a gidan kaso har na tsawon watanni 18 a masatyin jiran shari'a bisa zargin cin hanci.

Peru | Alejandro Toledo (picture-alliance/dpa/P. Aguilar)

Tsohon shugaban kasar Peru, Alejandro Toledo

Ana zargin tsohon shugaban da karbar cin hanci na dala miliyan 20 daga kamfanin aiyuka na kasar Brazil, kamfanin ya bada kudaden ne don a ba su damar gina babban titin da ya hada birnin Rio da Jenairo da kuma Lima. Masu gabatar da karar dai sun gabatar da shedu a gaban kotu da ke nuna almundahana da stohon shugaban ya aikata a tsakanin shekarun 2001 zuwa 2006, a lokacin ya na kan karagar mulki  sai dai bangaren Toledo sun ce za su daukaka kara.