1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a binciki tsohon shugaba Mugabe

April 20, 2018

Hukumomi a Zimbabuwe sun ce za su gayyaci tsohon shugaban kasar gaban majalisar kasa, domin ya amsa tamabayoyi kan badakalar wasu biliyoyin daloli da ake yi masa zamanin mulkinsa.

https://p.dw.com/p/2wPDY
Simbabwe Robert Mugabe 2008, Präsident
Tsohon shugaban kasar Zimbabuwe, Robert MugabeHoto: picture-alliance/AP Photo/T. Mukwazhi

Majalisar dokokin kasar za ta binciki tsohon shugaba Robert Mugabe, kan wani zargin sama-da-fadi da kudaden Lu'u-Lu'u mai karfi. Wannan ne dai bincike na farko da za a fara yi wa tsohon shugaban na Zimbabuwe da ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 37.

Shi dai Mr. Mugabe ya yi murabus daga mukaminsa ne cikin watan Nuwambar bara, sakamakon shiga da sojojin kasar suka yi bayan boren da al'umar kasar suka yi.

Ita dai badakalar ta Lu'u-Lu'un ta kai ta dala bilyan 15 wanda tsohon shugaban ya yi zargin an yi a wasu yankunan gabashin kasar, daga bisani kuma ya ce bai san da alkaluman ba. Majalisar dokokin kasardai ta ce dole ne Mr Mugabe ya yi masu bayanai a ranar 9 ga watan gobe na Mayu.