Za a aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris | Siyasa | DW | 18.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Za a aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris

Kasashen duniya sun amince da aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi da aka cimma a birnin Paris na Faransa a shekarar da ta gabata, a yayin taron sauyin yanayi da aka gudanar a Maroko.

Taro kan sauyi ko dumamar yanayin karo na 22 da ake wa lakabi da Cop 22 wanda ya hado kan shugabannin kasashe da ministocin muhalli da kungiyoyin fararen hula dana 'yan kasuwa da kuma masana kimiyya dai, a farko sun nuna fargaba kan abin da zaben sabon shugaban kasar Amirka Donald Trump ka iya haifarwa, inda suka yi tunanin ya na iya mai da hannun agogo baya wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a birnin Paris na kasar Faransa a shekarar da ta gabata, wadda ta amince da a rage yawan zafin da duniya ke fama da shi da digiri biyu a ma'aunin Celsius.

Wakilan Amirka a wajen taron da aka gudanar a birnin Marakesh na kasar Maroko sun tabbatar da cewa kasar za ta ci gaba da bin dukkan kudire-kudiren da aka amince da su a baya da kuma wadanda aka amince da su yanzu. Shugaban taron na bana kuma ministan harkokin kasashen ketare na Maroko Salaheddine Mezouar ya ce: "kudirin Marakash shi ne na tabbatar da kare muhalli da samar da ci-gaba mai dorewa kuma kasashe sun amince da hakan".

Shi kuwa a nasa bangaren wanda ya jagoranci tattaunawar kana jakadan Maroko a Majalisar Dinkin Duniya Aziz Mezouar ya ce tilas a hada hannu don rage hayakin da ke gurbata muhalli domin tabbatar da yarjejeniyar da aka cimma a Paris ta kai ga wanzuwa, inda ya kara da cewar: ''za´a fara gani a kasa na irin shawarwarin da aka amince da su kuma kasashe za su bada cikakken goyon bayansu don samar da makoma mai kyau".

Yarjejeniyar dai za ta tabbatar da cewa kasashen sun kimanta irin hayaki mai guba da suke fitarwa kana kasashen da suka ci gaba za su taka rawa wajen ganin sun taimakawa kasashe masu tasowa domin suma su bayar da tasu gudunmawar wajen rage dumama ko kuma sauyin yanayi a duniya baki daya.

 

A nata bangaren ministar muhalli ta kasar Jamus Barbara Hendricks da ita ma ta samu halartar taron sauyi ko dumamar yanayin a birnin Marrakesh na kasar Moroko, tare kuma da kaddamar da babbar tashar samar da hasken wutar lantarki da hasken rana a Morokon, cewa ta yi:


"Wannan shi ne sakamakon da muka samu a taron sauyi ko dumamar yanayi, kusan baki dayan al'umma sun san abin da ya kamata ke nan, hakan na nuni da cewa mutane ke haifar da sauyin yanyi. A bayyane yake karara cewa Jamus ba wai kawai jagora ce a duniya ba, harma cewa jagorace a batun sabunta makamashi a duniyar baki daya."
 

 

Sauti da bidiyo akan labarin