Za a ɗage ranar gudanar da zaɓe a Pakistan | Labarai | DW | 02.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a ɗage ranar gudanar da zaɓe a Pakistan

Jam´iyun adawa a Pakistan sun zargin gwamnati da jirkita zabukan da ake shirya gudanarwa a kasar don hana ta shan kaye.´Yan adawa sun nuna fargabar cewa wannan mataki ka iya haddasa karuwar tashe tashen hankula a cikin kasar wadda har yanzu take fama da rigingimu sakamakon kisan gillan da aka yiwa Benazir Bhutto. A jiya an jiyo wani babban jami´in hukumar zabe yana cewa hukumar ta amince ta dage ranar gudanar da zaben, inda ya yi nuni da cewa ba za a yi zaben ba har sai watakila a tsakiyar watan fabrairu, to amma yaki ya fadi takaimaimen lokaci gabanin sanarwar da za a bayar yau a hukumance. ´Yan adawa dai na zargin cewa hukumomin zasu dage zaben ne don taimakawa jam´iyar da ke jan ragamar mulki wadda ke kawance da shugaba Pervez Musharraf.