Zaɓen Zimbabwe | Siyasa | DW | 03.04.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaɓen Zimbabwe

Jinkirta fitar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Zimbabwe

default

Jami'an hukumar zaɓen ƙasar Zimbabwe.

Ganin cewa hukumar zaɓen kasar zimbabbwe ZEC ta Cigaba da yin shiru game da sakamakon kujerar shugaban ƙasa a zaben ƙasar Zimbabwe ta sanya 'yan adawa na cigaba da hasashen yin nasara a kan jam'iyyar gwamnatin maici a yanzu.

fitar da sakamakon sauran zaɓuka da hukumar zaɓen ƙasar Zimbabwen ta cigaba bai gamsar da al 'ummar ƙasar ba tare da sauran ƙasashen duniya tare da cewa jamiyar adawa ta MDC ita ce ke kan gaba,abin da aka matsu a gani shi ne sakamakon zaɓen shugaban ƙasa .

To ko wani ƙoƙari ƙungiyoyin kwadago da na fararen hula ke yi game da halin da ake ciki a zimbabwe ?Tambayar ke nan da Ita Mushekwe wani ɗan jarida kuma memba a ɗaya daga cikin irin waɗannan kungiyiyo ya amsa :

"Dokar Zimbabwe ta yi tsauri da yawa ta yadda ta baiwa shugaban ƙasa ƙarfi fiye da kima.Ƙungiyoyi a takure suke basu iya wani kataɓus.Muna dai fatan gani cewa idan aka kafa sabuwar gwamnati ta yi gyara a kundin tsarin mulkin ta yadda wannan fanni maimatukar mahimmanci ga rayuwar Dimokuraɗiyya za su riƙa tasiri."

Yanzu haka ma dai rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin 'yan ƙasar ta Zimbabwe na ta yin kaura zuwa ƙasar Afurka ta kudu domin gujewa ko kuma fargaban ɓarkewar rikici,ganin yadda sakamako da aka fitar ya ƙarawa 'yan adawa Kwarin gwiwar faɗin nasarar da suke ikirari daga farko wanda gwamnati ta bayyana da cewar ya sabawa dokar ƙasa.

A larabar nan babbar jamiyyar adawa ta MDC ta cigaba da kurarin yin nasara da samun kuru'u sama da kashi 51cikin ɗari ita kuma jamiyyar ZANU-PF mai mulkin kasar ta na da 48 cikin ɗari kacal.

A bisa dokar zaɓen kasar dai har sai ɗan takara ya sami kashi 51cikin ɗari na da kuri'un da aka kaɗa sannan ya yi nasara.A dongane da wannan ke nan ga dukkan alamu za a kai ga gudanar da zaɓe zageye na biyu a tsakanin manya jam'iyun biyu dake takara wato tsakanin shugaba Robert Mugabe da Morgan Tsvangarai.

Su kuwa masu fashin baƙi kan al'amuran yau da kullum suna bayyana hasashen cewa ne duk da cewar zaɓen zimbabwe ya gudana cikin kwanciyar hankali,to amma a bayyane take jinkirin da ake samu na fito da sakamakon zaben shugaban ƙasar na iya haifar da ƙazamin tashin hankali makamancin wanda ya biyo zaben ƙasar Kenya a watan Disambar bara ga ƙasar da jama'arta ke cikin ƙuncin tattalin arziki da tsadar rayuwa a kudancin Afurkan.