Zaɓen yan majalisun jihohi a Berlin da Mecklemburg | Siyasa | DW | 17.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaɓen yan majalisun jihohi a Berlin da Mecklemburg

Jam´iyar DCU ta sha kayi a zaben jihohin Berlin da na Mecklemburg

default

An kammalla yan Majalisun jihohin 2 na ƙasar Jamus da aka gudanar a yau lahadi.

Jihohin sun haɗa da Berlin babban birninTarayya, da kuma Mecklemburg-Pomerania, da ke arewa maso gabancin ƙasar.

A birnin Berlin mutane kussan milion 2 da rabi nwe ya cencenat su kada kuri´ar a wannan zabe sai kuma miliondaya da rabi a jihar Meck-Pom.

Wannan zaɓe na matsayin zakaran gwajin dafi, ga haɗin gwiwar jama´iyun CDU da SPD, da ke riƙe da ragamar mulki.

A duk tsawan lokacin yaƙin neman zaɓe yan takara daban-daban, sun bayana alkawura, da kuma husa´o´in su na magance matsalolin rashin aikin yi, da ƙara haɓaka tattalin arzikin jihohin.

Jihar Mecklemburg-Pomerania da ke matsayin ɗaya daga wuraren da jam´iyar CDU, ta Angeller Merkell ta samu karɓuwa, na sahun ƙarshe, ta fannin ci gaba, idan a ka jera jihohin 16 da Jamus ta mallaka.

A ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a kamin zaɓen ta nunar da cewa, Jam´iyar SPD zata samu rinjaye a birnin Berlin mussamman, saboda haskakar tarmamuwar magajin garin birnin Klaus Wowereit.

Sannan a jihar Mecklemburg-Pomerania CDU z ata shige gaban SPD, sannan jam´iyar yan Nazie ta NPD ita ma ,zata taka rawar gani.

Bayan bayana sakamakon zaben wannan hasashe ya zo daidai a birnin Berlin inda SPD ya zuwa yanzu ta samu kashi 31 da dudu 2 bisa 100 na yawan kuri´unda aka jefa ayayinda CDU ta samu kashi 21 da dugu 6.

Wannan na matsayin sakamako mafi muni da jamiýar Angeler merkell ta samu a birnin Taraya a tsawan tarihin ta.

Jami´yar the Greens ta samu kashi kussan 14 abirninBerlin, abinda ke matsayin gagaramar nasara a gare ta.

Shugaban jam´iya Roth Jubelt ya bayana gamsuwa da wannan sakamkako wanda zai basu damar shiga majalisar dokokin Berlin:

A jihar Mecklemburg-Pomerania jam´iyun SPD da na CDU sunyi kunen doki tarte da kussan kashi 30 bisa 100 na jimmilar ƙuri´un da aka jefa , sai kuma jami´yar yan Nazie ta NPD da ta samu fiye da kshi 6 bisa 100.

Wannan sakamako zai bata damar samun kujera a majalisar dokokin jihar, cemma NPD ta samu kujera a majalisar dokokin jihar Saxe da ke gabacin kasar a zaben shekara ta 2004.

 • Kwanan wata 17.09.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bty7
 • Kwanan wata 17.09.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bty7