Zaɓen yan majalisun dokoki a Poland | Labarai | DW | 21.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen yan majalisun dokoki a Poland

A ƙasar Poland, yau ne a ka gudanar da zaɓen yan majalisun dokoki.

A jimilce, mutane milion 30 da rabi ya cencenta suz ka kaɗa ƙuri´a, domin zaɓen yan majalisu 460 da majalasar Diete ta ƙunsa.

Jam´iyun adawa sun yi alkwarin samun gagaramin rinjaye, domin ƙwatar mulki, daga shugaban ƙasa Kazynski da abokin tagwaicin sa da ke riƙe da muƙamin Praminista.

Ƙiddidigar jin rajayin jama´a ,a gabanin zaɓen, ta nunar da cewa, akwai alamun yan tagwayen su sha kayi a wannan zaɓe.

Ƙasashen turai, mussamman Jamus, sun haƙe su samu sakamakon wannan zaɓe ta la´akari da rikicin da ke tsakanin ta, da gwamnatin ra´ayin riƙau,ta yan tagwayen Poland.

Rahottani daga Warso, babban birnin ƙasar, sun ce jama´a ta hito da himma, domin kaɗa ƙuri´a.

A na jiran sakamakon ƙarshe nan gaba a yau.