Zaɓen yan majalisun dokoki a Mali | Labarai | DW | 02.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen yan majalisun dokoki a Mali

Jama´ar ƙasar Mali, na cikin jiran sakamakon zaɓen yan majalisun dokoki zagaye na farko, da su ka gudanar jiya a fadin ƙasar baki ɗaya.

Rahottani daga sassa daban –daban na ƙasa, sun tabatar da cewa, zaben ya gudana lami lahia, to saidai a jama´aba ta hito da himma ba, a runfunan zaɓe, wanda su ka rufe ƙofofin su, a ƙarhe 6 agogon GMT.

Saidai a sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a yankin Segou, hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta umurci kammala zaɓen a karhe 10 a wannan yanki.

A jimilce, fiye da mutane milion 6, ya cencenta su ka kaɗa ƙuri´a, domin zaɓen yan majalisu 147, daga jimlar ya takara 1.400.

Masu sa ido kimanin 900 na ciki, da wajen Mali, su ka bi sau da ƙafa, yadda zaɓen ya wakana.

Ranar 10 ga watan mai kamawa majalisar mai ci yanzu ke sauka daga aiki.