Zaɓen ´yan majalisar dokoki a Curetiya | Labarai | DW | 25.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen ´yan majalisar dokoki a Curetiya

A yau ake gudanar da zaɓen ´yan majalisar dokoki a ƙasar Curetiya. Jam´iyar ´yan ra´ayin mazan jiya HDZ ta Firaminista Ivo Sanader na fuskantar ƙalubale babba daga manyan ´yan adawa na jam´iyar Social Democrats. Dukkan jam´iyun biyu sun yi alkawarin ɗaukar sahihan matakan yaki da cin hanci da rashawa, farfado da tattalin arziki tare da jagorantar kasar ta Curetiya zuwa cikin kungiyar tarayyar Turai EU. Masu sa ido sun ce babu ɗaya daga cikin jam´iyun guda biyu da zata iya kafa gwamnati ita kaɗai kuma za a ɗauki lokaci kafin jam´iyar da ta yi nasara ta kafa wata gwamnatin ƙawance. Ƙuri´ar jin ra´ayin jama´a da aka gudanar baya bayan nan ta ba wa jam´iyar social democrats karkashin jagorancin Zoran Milanovic wata tazara da ba ta taka kara ta karya ba.