Zaɓen shugaban ƙasar Ruwanda | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 13.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Zaɓen shugaban ƙasar Ruwanda

Kagame ya yi nasara ba tare da wata adawa ba

default

Shugaban Ruwanda Paul Kagame

Za mu fara ne da ƙasar Ruwanda. A labarin da ta rubuta mai taken gagarumar nasara ba tare da adawa ba, jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi kamar yadda aka yi hasashe an sake zaɓan shugaba Paul Kagame na Ruwanda bayan tun farko an mayar da 'yan adawa tamkar saniyar ware a zaɓen. Sake zaɓensa dai na nufin kenan Kagame zai ci-gaba da mulkin ƙasar shekaru bakwai nan gaba. Jaridar ta ce ko da yake shugaban ya jaddada cewa zai ci-gaba da aiwatar da kyawawan manufofin ta da komaɗar tattalin arzikin ƙasar tare da janyo hankalin masu zuba jari na ƙetare amma matsalar kamar yadda masana suka nunar ita ce, wannan ci-gaban a babban birnin ƙasar wato Kigali ne kaɗai yayi tasiri, mazauna yankunan karkara sai ƙara talaucewa suke. Sannan har yanzu ana nuna rashin gamsuwa game da sasanta al'umma bayan kisan ƙare dangin 1994. Jaridar ta kwatanta Ruwanda da wata ƙasa dake rawa akan wani dutse mai aman wuta.

Ruanda Präsidentenwahl Stimmabgabe in Kigali

Koma baya ga shugaba Kagame inji jaridar Tageszeitung tana mai nuni da kashi 93 cikin 100 na yawan ƙuri'u da ya samu. Ganin yadda 'yan adawa ke da rauni a ƙasar. Kagame ya yi hasashen cewa zai samu sama da kashi 100 cikin 100 na yawan ƙuri'u.

Ita kuwa jaridar Die Welt ta mayar da hankali ne kan shari'ar da akewa tsohon shugaban Laberiya Charles Taylor a birnin The Hague, inda mashahuriyar mai sanya kayan zamani Naomi Campbell ta ba da shaida game da lu'ulu'un da Taylor ɗin ya ba ta. Jaridar ta ce duk da bayanai saɓanin juna da Naomi Campbell da Mia Farrow suka bayar a gaban kotu, an cimma abu ɗaya, wato rawar da Taylor ya taka a yaƙin basasan ƙasar Saliyo ta fito fili.

Niederlande Kriegsverbrechertribunal Den Haag Naomi Campbell

Naomi Campbell a akwatin telebijin lokacin da take ba da shaida a Kotun duniya ta birnin The Hague

To sai dai jaridar ta ce ai ba a Saliyo kaɗai aka yi fama da yaƙin basasa ba, daga shekarar 1996 zuwa 2003 mutane miliyan biyar a Kongo sun rasa rayukansu sakamakon yaƙin da aka yi don mallakar ma'adanar ƙarƙashin ƙasa kamar sinadarin Coltan wanda ake amfani da shi wajen harhaɗa wayar salula. Buƙatar da ƙasashe masu ci-gaban masana'antu ke da ita ga ɗanyun kaya na daga cikin dalilan dake janyo rigingimu a Afirka. A saboda haka, inji jaridar, ya zama wajibi ƙasashen masu ci-gaba su san da wa suke gudanar da ciniki da kuma tasirinsa da al'ummomin ƙasashen da ake hulɗar cinikin da su.

Har yanzu ƙasar China na ci-gaba da faɗaɗa haɗin kai da ƙasashen Afirka domin tabbatar da samun ɗanyun kaya, inji jaridar Neues Deutschland inda ta ƙara da cewa Chinar na yin haka ba tare da tsoma baki a harkokin siyasar nahiyar ba. Daga shekarar 2000 zuwa 2008 harkokin cinikaiya tsakanin China da Afirka sun ruɓanya daga dala miliyan dubu 10.6 zuwa miliyan dubu 106.8. Yanzu haka ƙasar ta China ta fara horas da ƙwararrun Afirka kimani 15000 a fannoni daban daban yayin da ita kuma ta tura ƙwararrunta na aikin noma domin horas da 'yan Afirka sabbin dubarun noma.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu