1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasar Abirkos

Yau hukumar zaɓen Abirkos ke raba katuttukan zaɓe a Abidjan.

default

Birnin Abidjan

Hukumar zaɓen Abirkos ta ce a yau ne za ta raba katukkukan zaɓe a birnin Abidjan da ke zaman cibiyar kasuwancin ƙasar, kafin zaɓen shugaban ƙasar da zai gudana a ranar 31 ga wannan wata na Oktoba. Tun daga shekarar 2005 ne ake ta dage wannan zaɓe sakamakon takaddamar da ta taso bisa wanda ya cancanci ya kaɗa ƙuri'a da kuma kwance wa yan tawaye ɗamarar yaƙi. Ana kyautata fatan cewa wannan zaɓe zai kawo ƙarshen rigingimun da ake ci gaba da samu a ƙasar sakamakon yaƙin basasan da ta fuskanta daga shekarar 2002 zuwa 2003, a baya ga kawo canji ga aikin nomar koko a ƙasar da ke samar da kashi guda bisa uku na kokon da ake bukata a duniya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu