Zaɓen shugaban ƙasa zagaye na 2 a Benin | Labarai | DW | 19.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa zagaye na 2 a Benin

A Jamhuriya Benin,a na ci gaba da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na 2.

Kimanin mutane million 4 su ka koma runfunan zaɓe, kwanaki 2 rak, bayan bayyana sakamakon zaɓen zagaye na farko da a ka gudanar ranar 5 ga watan dam u ke ciki.

Daga jerin yan takara 26, da su ka shiga zagayen farko ,2 ke fafatawa a wannan karo, wato Yayi Bonny, tsofan daraktan bankin ƙasashen yammacin Afrika ,BOAD, a matsayin ɗan Independa, sai kuma Adrien Houngbeji ,tsofan shugaban majalisar dokoki, kuma tsofan Praminista.

Sakamakon da hukumar zaɓe mai kanta ta bada, a zagayen farko, ya ba Yayi Boni ,kashi kussan 36 bisa 100 ,na yawan ƙuri´un da a ka kaɗa, sannan Adrien Houngbeji ya zo na 2, tare da fiye da kashi 24 bisa 100.

An fuskanci saɓanin ra´ayoyi, tsakanin hukumar zaɓe mai zaman kanta, da fadar shugaban ƙasa, a dangane da ranar shirya zagaye na 2 na zaɓen.

Wannan saɓani bisa dukkan alamu, zai sa a shirya zaɓen na yau,a karmatse, ba tare da yan takara 2, sunyi yaƙin neman zaɓe ba.

Saidai, a nasa gefe Yayi Bonny, ya samu goyan baya, daga yan takara 3, a zagaye na farko, wanda baki ɗaya, su ka haɗa kashi 28 da yan ka, na yawan ƙuri´un da a ka jefa.

Ya zuwa yanzu, rahotanin da mu ka samu, na nuni da cewar a na gudanar da zaɓen lami lahia.