Zaɓen shugaban ƙasa a Rwanda | Siyasa | DW | 09.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaɓen shugaban ƙasa a Rwanda

Zaɓen shugaban ƙasa irinsa na biyu tun bayan kisan kare dangi a Rwanda a shekarar 1994

default

Wata mace a Rwanda yayin da take kaɗa ƙuriarta a rumfar zaɓe

Duk da cewa an yi hasashen cewa Paul kagame zai samu damar yin tazarce, amma kuma kungiyar gamayyar Turai ba ta aika da masu sa ido ba.

Tun dai da jijjibin safiyar wannan litinin ne, dubun dubatan 'yan kasar ta Rwanda suka yi cincirindo a gaban runfunan zabe sama da dubu 15 da aka tanadar domin kada kuri'a. Har ya zuwa yanzu, ba a sami rahotannin barkewar wani rikici ko kuma kunnowar wata matsala ba. A daura da haka ma dai, kamalla kada kuri'ar aka yi cikin gamo da kasawa a wasu mazabun musamman ma na lardin yammacin kasar ta Rwanda. Galibinsu kuma na nunawa cewa Paul Kagame suka zaba. dama tun bayan da aka 'yan koransa uku ne suke kalubakantarsa, masana suka yi hasashen cewa babu makawa, shugaban mai shekaru 52 da biyu zai samu damar yin tazarce. A lokacin da aka yi masa tambaya game da rashin tsayawa takaran 'yan adawa na fil azam na kasar, kagame tsakaci yayi da cewa

"Aiki da ke gabana, ba kirkiro da adawa ba ne. Amma kuma abin da ya kamata in yi shi ne in dauki matakan da suka tabbatar da cewa ba a tafka magudin ba."

Ruanda Präsidentschaftswahl 2010 Afrika Kigali Paul Kagame

Shugaban Ƙasar Rwanda Paul Kagame

Masu sa ido na kungiyar gamayyar Afirka da kuma Commonweath har guda dubu da 400 ke barbaje a fadin kasar ta Rwanda domin shaidar da sahihancin zaben. sai dai kungiyar gamayyar Turai ba ta aike da masu sa idonta ba, saboda matsalolin kudin da ta ce tana fiskanta. Amma kuma masu lura da harkokin siyasar kasa da kasa na danganta wannan mataki na EU  da bacin kudi da lokaci, saboda tabbaacin da ake da shi cewa kagame zai lashe zaben. sai dai 'yan adawan kasar sun nunar da cewa kaurace ma ma zaben da Eu ta yi, alama ce da ke nuna rashin jin dadinta da tauye hakkin jama' a da gwamnati ta ke yi. frank Habineza na daya daga cikinsu

"Babu demokaradiya a wannan kasa. Babu 'yancin fadan albarkacin baki. Ba a sakar ma 'yan jarida mara. Kuma babu 'yancin gudanar da taro na siyasa. kai shiga cikin wata jam'iya baya ga ta gwamabti, daidai ya ke da kisan kai."

Sai dai Kagame ya sakafa ya fatali da zargin da ake yi masa na tauyen hakkin bil adama. Maimakon haka yana mai alfari da dora kasarsa kan turbar da ya sa ta zama sha yabo a cikin da wajen Afirka. Tattalin arzikinta na daga cikin wadanda suka fi murmurewa a Afirka. Cin hanci da karbar rashawa ya kusan zama tarihi a Rwanda. Yayin da kuma a daya hannun, magani da kuma matakin karatu na firamare, ake ba dawa kyauta ga 'yan kasar a tsohon shekaru 10 na mulkin Paul kagame. Ya kuma yi alkawarin sauka idan ya sha kayi a zaben na wannan litinin

"Idan al'umar kasar Rwanda suka ki sabontamin wa'adin muli, to lallai zan mutunta wannan zabi nasu da kashi 110 bisa 100."

Sai dai harin gurneti da aka fiskanta a kwanakin baya a kasar ta Rwanda, da kuma guna-gunin da wasu masu fada a ji na kabilar tutsi ke yi , sun sa ana ganin akwai afkuwar rikici a zaben na wannan litinin.

Mawallafi : Mouhammad Awal Balarabe Edita : Abdullahi Tanko Bala