Zaɓen shugaban ƙasa a Poland | Labarai | DW | 20.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa a Poland

Al'umar Poland na kaɗa ƙuri'a domin zaɓar sabon shugaban ƙasa.

default

Jaroslaw Kaczynski, ɗan takarar jam'iyar yan mazan jiya

A yau al'umar ƙasar Poland ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa domin maye gurbin shugaban ƙasar Lech Kaczynski wanda ya rasu a haɗarin jirgin sama a watan Aprilu. Ɗan uwan tagwaitakarsa Jaroslaw Kackzysnki na jam'iyar 'yan mazan jiya na cikin takara dake neman kujerar shugabancin ƙasar. Sai dai kuma ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni da cewa yana bayan ɗan takara adawa Bronislav Komorowski. 'Yan takara goma ne ke fafatawa a wannan zaɓe. Idan babu wanda ya sami kashi 50 cikin 100 za'a koma zagaye na biyu a ranar huɗu ga watan Juli. Ɗan takarar adawa Bronislav Komorowski mai ra'ayin tarayyar Turai ya yi alƙawarin idan ya yi nasara zai shigar da ƙasar cikin rukunin ƙasashe masu amfani da kuɗin bai ɗaya na Euro a shekaru biyar. A matsayinsa na shugaban majalisar dokoki ya karɓi ragamar riƙon ƙwarya bayan rasuwar shugaba Kackzynski a haɗarin jirgin sama.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Mohammad Nasiru Awal