Zaɓen shugaban ƙasa a Kolambiya | Labarai | DW | 30.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa a Kolambiya

Al´umomin ƙasar Kolambiya sun fito domin zaɓen shugaban ƙasa daga jerin ´yan takara tara

default

Biyu daga cikin ´yan takara zaɓen shugaban ƙasar Kolambiya

Kimanin mutane miliyan 30 ne, ya cencenta su fito yau a ƙasar Kolambiya domin zaɓen shugaban ƙasa daga jerin ´yan takara guda tara. Idan babu ɗan takara da ya samu gagaramin rinjaye a zagayen farko, za a shirya zagaye na biyu ranar 20 ga watan mai kamawa.

A zaɓɓuɓukan shekara ta 2002 da 2006 shugaba mai barin gado Alvaro Ulribe yayi nasara tun zagayen farko.Amma a wannan karo dokokin ƙasar sun haramta mashi sake ajje takara. Yayi ƙoƙarin yin kwaskwarima ga kudin tsarin mulki ba tare da cimma nasara ba.Ana gudanar da wannan zaɓe cikin tsatsauran matakan tsaro.A jajibirin wannan zaɓe mutane huɗu sun rasa rayuka a cikin rikece-rikice daban-daban.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi