Zaɓen shugaban ƙasa a Gambia | Labarai | DW | 22.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa a Gambia

Yau ne al´ummar Gambia dake yammacin Afrika, ke zaɓen shugaban ƙasa.

A jimilce mutane dubu 670 ne, ya cencenta su kaɗa ƙuri´u a cikin mazaɓu kimanin dubu ɗaya, a faɗin kasar baki ɗaya.

Shugaban ƙasa mai ci yanzu, Yahaya Jameh, mai shekaru 41 a dunia, na daga sahun yan takara 3 da su ka shiga wannan zaɓe.

Tunni al´ummomin ƙasar sun tabbattar da cewa, za shi tazarce, ta ko wane hali.

Shi da kansa ya ce bai ga abinda zai hana masa ci gaba da mulkin ƙasar Gambia ba, har nan da tsawon shekaru 40 masu zuwa indai da rai da lahia.

Yan takarar 2 su ne, Usainu Darboe na jam´iyar UDP, sai kuma Halifa Salah na hadin gwiwar jam´iyu 3 NADD.

Yahaya Jameh ya hau karagar mulkin ƙasar Gambia tun shekara ta 1994 bayan juyin mulkin da yayi wa Dauda Jawara.

Sannan ,an shirya zaɓe a shekara ta 1996, inda yayi tazarce, ya kuma ƙara zarcewa a shekara ta 2001.