Zaɓen shugaban ƙasa a France | Labarai | DW | 22.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa a France

Saɓanin Nigeria, inda zaɓe ya wakana cikin rashin tsari, a France, yau ne al´umommin ƙasar, na ciki da na waje, su kimanin milion 45, ke zaɓen shugaban ƙasa, zagaye na farko, cikin kwanciyar hankali da lumana.

Yan takara 12, su ka shiga wanan zaɓe, to saidai 4 da ga cikin su ne a ke kyauttata zaton,za su kai labarai, zuwa zagaye na 2,wanda za a shirya ranar 6 ga watan Mayu mai kamawa.

Wannan yan takara sun haɗa da Nicolas Sarkozy na jam´iyar UMP, mai riƙe da ragamar mulki, da Segolene Royale, ta jama´iyar Gurguzu, sannan Fransois Bayrou, na jam´iyar UDF mai matsakaicin ra´ayi, da kuma Jean Marie le Pen, na jam´iyar FN mai aƙidar wariya, wanda kuma ya zo zagaye na 2, a zaɓen shekara ta 2002.

Ya zuwa yanzu rahottanni daga sassa daban-daban na ƙasar sun ce jama´a ta fito da himma, fiye da zaɓen da ya gabata domin kaɗa ƙuri´a.

Baki karfe 7 daidai agogon Nigeria da Niger, za a rufe ruffunan zaɓe, kuma, a na sa ran fara sakamakon farko tun daga ƙarfe 8 na yammacin yau.